Maganin Gargajiya

Hanyoyin Rabuwa Da Istimna’i Cikin Ikon ALLAH

Maganin Gargajiya

 

Hanyoyin Rabuwa Da Istimna’I Cikin Ikon ALLAH

Kamar Yadda kuka sani Istimna’i Wato Zinar Hannu Yana Mugun Illata muna Lafiyarmu ta hanyoyi mabanbanta toh Alhamdulillah yau mun kawo muku wasu hanyoyinda inkukabi insha ALLAH zaku rabu da illolin istimna’i cikin yardan ALLAH. mai karatu biyomu cikin wannan karatu domin ganin yadda zaka rabu da wannan matsala.

MUNA DA MAGANIN ISTIMNA’I, ( IDAN AN DAINA ):

Idan ALLAH Yabaku ikon daina istimna’i Munada maganin wanda zai wanke muku wannan cuta cikin yardan allah

Hakika matsalar Istimna’i (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu’a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.

Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba’ira bane!!

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala’in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna’i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.

Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna’i, da sauransu.

Kamar yadda muka sha fada, Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala’in sun hada da:

Ga Jerin Yadda Zakubi Domin Rabuwa Da Wannan Cuta

  1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)
  2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
  3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.
  4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.
  5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
  6. Yawaita karatun Alqur’ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.
  7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
  8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.
  9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.
  10. Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke Qunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar Friends masu sharing din irin wannan.

Mustapha Lamszxy

Blogger | Disc Jockey | Distributor | Developer | Typist | Advertiser

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button