Maganin Gargajiya

Illar Istima’i Ga Matasa

Maganin Istimna'i

 

Illar Istima’i Ga Matasa

Kusan Yawancin Samari Da Yan Mata Musmman Ga Yaya Maza Wato Samari Kaso 90% Cikin dari Suna Aikata Istimna’i Wato Zinar Hannu A Turance (Masturbation) Domin Biyawa Kansu Bukata Na Sha’awa Harda Su Mata Suma Mafi Yawancinsu Suna Aikata Wannan Domin Biyawa Kai Bukata Ta Hanyar Wasa Da Wani Abu Zuwa Farji Da Dai Sauransu.

Kuma Wannan Ba Karamin Illa Bace Ga Rayuwarsu Baki Daya Domin Istimna’i Yana Janyo ABubuwa Kamar Haka.

  1. Rashin Haihuwa
  2. Yawan Mantuwa
  3. Yayan Tunani
  4. Yayan Ramewa
  5. Kankanchewar Azzakari
  6. Karancin Sha’awa Da Dai Sauransu.

Masturbation:

Shi ne Wasa da Al’aura, wanda a larabce aka sansa da “Istimna’i” Wannan yana nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima’i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji, ga mace. Wasa da Al’aura ga maza, sukan yi amfani da Sabulu ko Mai ko wani abu mai yauki da santsi ta hanyar mulmula Azzakarinsu har su biya bukatar su. Amma mata, suna amfani da yatsa ko kyandir ko wani abunda za su tura cikin gabansu, har su biya bukatar su.

Ya ‘yan uwa, wannan matsala ta Wasa da Al’aura, dabi’a ce abin kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan addini, na al’ada, da kuma na lafiya.

Malaman Musulunce sun tafi akan HARAMCIN Wasa da Al’aura don biyan bukata, dalilin fadan Allah (SWT): ‘Da wadanda suke, gafarjojinsu, masu tsarewa ne. Sai fa akan matansu… To, duk wanda ya nemi abinda yake a bayan wannan, to, wadannan su ne masu ketare iyaka’ (Mara’rij 29 – 31, Muminun 2- 4), ‘ Kuma wadannan da ba su samu aure ba, sukame

kansu har Allah ya wadatar da su daga falalarsa… (Annur 33)

Haramcin wannan dabi’a ta Wasa da Al’aura, fahimta ce ta manyan malaman duniya, kamar Malikiyya, Shafi’iyya, Hambaliyya, Shi’a, Ibn Taimiyya, Ibn Kayyim, Ibn Baz, Usaimin…

Dukkan Musulmi an umurce shi da ya yi aure, in ba zai iya ba, yayi Azumi, Kuma ya tsare idonsa da kunninsa da ga kallo ko sauraren batsa da al-fasha. Musulunci ya yi umurni da haka ne tare da karanta cin abinci don rage sha’awa.

Lokacin da bawa ya bi dukkanin hanyoyin da muka ambata don tsare kansa da ga zina, amma ya kasa samun saukin sha’awar sa, to, Malamai suna ganin idan yayi Wasa da Al’aurar sa don gudun fadawa ga halakar Zina, to, ba bu laifi akan sa, sabo da lalura.

Duk da yake dai malamai sunyi sauki akan mas’alar Wasa da Al’aura (istimna’i) don biyan bukata, sa bo da lalurar tsananin sha’awa.

Binciken masanan kimiyyar lafiya ya nuna cewa YAWAN WASA DA AL’AURA (excessive masturbation) nada illa ga lafiya. Kuma ya zama matsala ga magidanta, don wasu har bayan aure ma suna yi, don ba su samun gamsuwa, sai sun yi abinan da suka saba da shi, wato, Wasa da Al’aura (istimna’i).

A shari’ance kuwa, shari’a za ta hukunta duk wanda aka sa me shi da wannan laifi. Kuma shari’a ta wajabta tuba a gareshi. Allah ya tsare bayin sa da ga dukkan mummunar dabi’a. Amin.

Allah she ne mafi sani.

Mustapha Lamszxy

Blogger | Disc Jockey | Distributor | Developer | Typist | Advertiser

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button