Maganin Gargajiya

Illolin Masturbation Wato Istimna’i

Maganin Istimna'i

 

Illolin Masturbation Wato Istimna’i

Wato Istimna’i Kokuma Masturbation Yana Matukar Illata Samari Da Yan Mata Wadanda Basada Aure Harda Masu Aure Suma Inhar Suna Aikata Toh Yana Illatasu ka kasance tareda mu domin jin sauran bayanan dakuma yadda zakayi ka guje aikata istimna’i

Masturbation ko kuma Istimna’i, wato wasa da tsiraici don biyawa kai bukatar jima’i.

Masturbation ko kuma Istimna’i a larabce, wata hanya ce da mutum kan bi don biyawa kansa bukatar sha’awa irinta aure.

Wasu sukan yi amfani da hannunsu ko wasu sassa na jikinsu, wasu kuma sukan yi amfani da injina ko sauran abubuwa da aka kera musamman don ay wannan lalata da su.

Masturbation ya zama ruwandare game duniya a tsakanin musamman matasa, wanda shi ne babban bala’in da ya ke lalata rayuwar matasa a wannan lokaci, ya 6ata rayuwar matasa da yawa maza da mata.

Anan muna so ne muyi bayanin illolin Masturbation da kuma hukuncin Mai yinsa a addinin musulunci, duk da dai wasu Malaman sun ce duk Mai Yin Istimna’i za a tashe shi ranar Alqiyama ya yi wa hannunsa ciki.

Kafin in kawo illolin Masturbation, bari in yi bayanin wasu daga cikin abubuwan da ke jefa matasa har da ma wasu masu auren cikin wannan bala’i.

 1. Wasu daga matasan ‘yan uwansu ne matasa suke ziga su su fara, ta hanyar cewa yin hakan yana maganin wasu cututtuka kamar ciwon ciki, ko maganin mataccen maniyyi, Wanda wannan karya ce kawai.
 2.  Wasu kuma Shaidanun kansu ne suke sa su, inda Shaidan zai ce musu ‘Ai da kay zina gara kay
 3. wannan, tunda ba ‘yar kowa ka 6ata ba’. Wanda wannan ma shirme ne da toshewar basira.
 4.  Wasu masu auren an ce musu Masturbation yana Kara tsawon gaban najimiji, don haka suke yi amma daga karshe za suy nadama, don kuwa gabansu zai karye, ya daina tashi kwata-kwata.
 5. Kallon hotunan tsiraici da zantuttukan batsa da wasu matasan sukan yi, har ma da karanta mujallu na batsa.
 6. Musamman mata, akwai wadanda ba sa jin kunyar bude tsaraici a gaban ‘yan uwansu mata, suna ganin kamar ba komai tunda dukkansu mata ne, hmm!, wasu matan ma har a mota suke ba yayansu nono ko makaranta ko a kasuwa, ba tare da sun ke6e inda maza ba za su gan su ba. Hakan na iya tayar da sha’awar wasu kuma ga shi ba su da aure don haka za su iya fadawa zina ko suy Istimna’i.
 7. Akwai ‘yan matan da suke son aure, amma iyayensu sun ce karatu za suy,ga shi kullum littatafan aure da soyayya ake karanta musu ta gidan rediyo da kuma fina-finan soyayya da suke kallo.

Akwai kuma maza masu son aure amma ba su da sana’a ko aikin yi, kuma dukkan danAdam baligi Mai lafiya yana da sha’awa, don haka za su iya fadawa harkar Masturbation.

Wannan su ne wasu daga cikin abubuwan da ke jefa matasa a wannan tsautsayi. Da fatan Allah ya kiyaye mu.

READ ALSO: Illolin Istimna’i Da Kuma Maganinsu

WASU DAGA ILLOLIN MASTURBATION

 

Yana janyo:-

1. Yawan mantuwa. Duk mai wannan aiki zai gamu da yawan mantuwa da shiririta.

2. Yana rage hazaqar kwalwa. Duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya dena fahimta.

3. Kankancewar gaba da

maraina ya koma kamar na yaro karami ko ya tattare ya dinga komawa ciki.

4. Saurin kawowa yayin jima’i. Wani ko minti daya ba ya iya yi, yayin tarawa da iyalinsa sai ya ji ya kawo kuma ba zai iya komawa ba.

5. Ramewa. Mutum zai ta ramewa, komai cin abincinsa da shan magunguna kara kiba.

6. Rashin karfin mazakuta har ta kai in yay aure ba ya iya gamsar da iyalinsa.

7. Mazakutar namiji tana iya karyewa, ya zama kwata-kwata ya dena tashi, sedai ya dinga dan motsawa kadan.

8. ‘Karancin sha’awa bayan aure.

9. Karancin maniyy. Wanda hakan yake da illoli da yawa, kamar haifar da rashin gamsar da iyali, rashin iya haihuwa da dai sauransu.

10. Raunin jiki, duk mai yin masturbation yanay wa jikinsa asarar wasu sinadarai masu kara kuzari. Don haka zai zama mai raunin jiki.

11. bushewar fatar kan zakari ya dinga wani abu kamar 6awo ko `kanzo.

12. Tsargiya, fitsarin jini. Yin masturbation kan sa mutum ya ga yana fitsarin jini, ko in yay masturbation din ya ga ya taho har da jini.

13. Watery sperm. Yana sa maniyyin mutum ya tsinke ya zama kamar ruwa kuma mara kauri, wanda hakan ke nuna dakyar in mutum zai iya haihuwa.

14. Yana sa mutum haka kawai ya ji yauqi yana fito masa koda bai yi masturbation din ba.

15. Idan masturbation ya ratsa mutum, to in bai yi ba ba zai iya bacci ba.

16. In ya sarqi mutum to in ya kwana biyu bai yi ba sai ya yi ciwon ciki kamar zai mutu.

17. Mace mai yin masturbation yana jawo mata doyin farji. Wato jin wari yana fitowa ta gabanta.

18. Ganin wani farin ruwa yana fitowa.

19. Kaikayi da kurajen gaba.

20. Yana kawarwa da mace budurcinta.

21. Yana kawo zubewar nono ga mace.

22. Yana sa mace ta dena sha’awar namiji samsam.

23. Koda mutum yay aure in ya tara da iyalinsa to se ya kara da masturbation sannan yake samun cikakkiyar gamsuwa. Idan mace ce ma haka.

24. Yana iya sa wa idan mutum ya girma ya kasa rike fitsari.

25. Masturbation hanya ce ta afkawa cikin zina da madigo da makamantansu.

26. Yana rage lafiyar idanu.

HUKUNCIN MASTURBATION A ADDININ MUSULUNCI:

Imam Malik Imam Shafi’i.

Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

Imam Abu hanifa.

Shi kuma ya tafi akan halas ne amma da sharadi, sharadin kuwa shine Sai in sha’awa ta tasoma mutum kuma sha’awar tazo ne kurum daga Allah ba wai mutum da kansa bane ya kirkiri hanyar zuwan sha’awar da kansa ba.

To anan Imma abi haneefa yace halas ne mutum yayi

 

ISTIMNA’I.

Imam Ahmad bin hanbal.

Shi kuma ya tafi akan cewa halas ne kuma babu wani sharadi don haka a gunsa ya halatta ka iya kirkiro sha’awar da kanka kuma kaji dadi ta hanyar istimna’i. Hujjarsa itace da mutum yayi zina gara yayi hakan.

HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION

 1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici.
 2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
 3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.
 4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.
 5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
 6. Yawaita karatun Alqur’ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.
 7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
 8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.
 9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar

Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.

10. Yawaita yin Azumi, domin garkuwa ne.

GA WASU HANYOYIN:

Idan ba ka da aure kuma sha’awa na damunka ko damunki sai ka:-

Dinga cin abinci wanda aka sarrafa da WAKEN-

SUYA (soya bean) yana rage sha’awa.

NA’A-NA’A

(pepper mint/mint) nada amfani ga lafiya sosai, toh amma itama ‘dan’danon ‘mint’ (menthol) da take dashi yana dakushe sha’awa.

Ka jika Kanwa ka matsa lemon tsami kadan a ciki ka sha, shi ma yana rage sha’awa.

Idan kuma kana da aure to:-

Ka dinga markada Gurji wato Cocomba kana yin lemo da shi, wannan yana kara yawan sperm.

Ka dinga cin Muruci, yana karawa maza karfin jima’i.

Yana da kyau ka ziyarci likita in har wannan matsala ta ci karfinka, ko kaziyarce mu mu hada maka magani, mata da maza. Muna kuma hada magungunan ni’ima da gyaran jiki na mata da magungunan karya sihiri da sharrin Aljanu.

Mustapha Lamszxy

Blogger | Disc Jockey | Distributor | Developer | Typist | Advertiser

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button