
Umar M Shareef – Tafiya Ta
Fitaccen mawakin Kannywood, Umar M Shareef, ya sake bayyana fasaharsa ta musamman a cikin sabuwar wakarsa mai taken “Tafiya Ta.” Wannan waka tana cikin kundin wakokinsa (album) mai suna “Ni Da Ke EP”, wanda ya ƙunshi wakoki 18 masu cike da soyayya da nishaɗi.
Wakar “Tafiya Ta” ta ƙunshi saƙon soyayya da taɓa zuciya, inda Umar M Shareef yake bayyana yadda tafiyar soyayya ke da wahala amma kuma cike take da ƙauna da fatan alheri. Muryarsa mai daɗi da lafuzan da suka dace sun sa wakar ta zama ɗaya daga cikin wakokin da masoya ke yawan saurare.
Stream Download Share



