Danmusa New Prince – Garkuwar Matan Hausa

Danmusa New Prince – Garkuwar Matan Hausa
Fitaccen mawakin Arewa Danmusa New Prince ya sake dawowa da sabuwar waka mai taken “Garkuwar Matan Hausa”, wacce ta haɗa nishaɗi, yabo, da salo na musamman. Wannan waka ta tabbatar da irin ƙwarewar Danmusa a fagen Hausa music, musamman wajen haɗa kalmomi masu ma’ana da kidan da ke taɓa zuciya.
A cikin wakar, Danmusa New Prince yana bayyana girmamawa da yabo ga mata, yana kiran su “Garkuwar Matan Hausa” wato ginshiƙai masu daraja da kima a cikin al’umma. Wakar ta ƙunshi kalamai masu kyau da sauti mai daɗin sauraro wanda ke nishadantar da duk mai sauraro.
Recommended: Usman bee Ft. YoungCee – Ga Labubu
“Garkuwar Matan Hausa” ta zama ɗaya daga cikin wakokin da ake yawan ji a TikTok, YouTube, da sauran kafafen sada zumunta saboda sautin kidanta mai motsa rai da muryar Danmusa mai ƙarfi da natsuwa.



